Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-07-29 15:46:25    
Za a iya yin amfani da dukkan dakuna da filayen motsa jiki na gasar Olympic ta Beijing

cri

Bayan da aka bude kofar unguwar 'yan wasannin motsa jiki ta gasar Olympic ta Beijing a kwanan baya, kungiyoyin wakilan 'yan wasa na yankuna daban daban na duk duniya sun soma isowa birnin Beijing bi da bi. Bayan isowarsu a Beijing, ko shakka babu abin da ya fi muhimmanci shi ne za su shiga dakuna da filayen motsa jiki domin kara yin horaswa kafin kaddamar da gasar Olympic ta Beijing a hukunce. Amma ya zuwa yanzu ko an riga an kammala dukkan ayyuka na dakuna da filayen motsa jiki fiye da 30 da ake samar wa gasar Olympic ta Beijing? A ran 27 ga wata, wato a ranar da aka bude kofar unguwar 'yan wasa ta gasar Olympic ta Beijing, wakilanmu sun gano cewa, yanzu dukkan dakuna da filayen motsa jiki na gasar Olympic ta Beijing suna cikin halin da za a iya yin amfani da su a kowane lokaci. Madam Wang Tongjie, wadda ke kula da gasar wasan lankwashe jiki a dakin wasan motsa jiki na kasar Sin ta gaya wa wakilinmu cewa, kungiyar kula da wasan lankwashe jiki ta kasa da kasa ta yaba wa ayyukan share fagen gasar lankwashe jiki da aka yi a dakin wasan motsa jiki na kasar Sin.

"Jiya wani jam'in kungiyar kula da gasar wasan lankwashe jiki ta kasa da kasa ya iso nan Beijing domin binciken na'urorin da za a yi amfani da su a gun gasar. Ya riga ya yi bincike kan na'urorin wasan lankwashe jiki iri iri, kuma ya nuna farin cikinsa game da wadannan na'urori. Bayan da wannan jami'i ya amince da ingancin na'urorinmu, za mu iya fadi cewa, mun riga mun gama dukkan ayyukan share fagen gasar cikin nasara."


1 2 3 4