Aminai 'yan Afrika, ko kuna sane da cewa, tun daga farkon wannan wata ne, masu aikin sa kai na gasar wasannin Olympic ta Beijing suka yi aiki kan gurabensu. Yau Laraba a nan Beijing, Madam Zhang Hong, mataimakiyar minista mai kula da harkokin masu aikin sa kai na kwamitin shirya wasannin Olympics na Beijing ta sanar da cewa an rigaya an kammala ayyukan share fagen gasar wasannin Olympic.
Jama'a masu sauraro, akwai masu aikin sa kai kimanin 100,000 da za su bada hidimomi kai tsaye a lokacin gasar wasannin Olympic ta Beijing da kuma gasar wasannin Olympic ta nakasassu na Beijing. Ban da wannan kuma akwai masu aikin sa kai kimanin 400,000 da za su gabatar da labarai, da yin tafinta da kuma bada tallafi da ceto cikin gaggawa a cikin birane da kuma wuraren da ke kewayen filaye da dakunan wasannin Olympics. Madam Zhang Hong ta furta cewa : 'Har kullum muna mai da hankali sosai kan tattara jama'a da dama don su shiga harkokin wannan gagarumar gasa. Kuma muna fatan masu aikin sa kai za su kara sajewa cikin ayyukan hidimomi '.
1 2 3 4
|