Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-06-19 14:03:18    
Kiyaye zaman lafiya cikin wahala kuma da jin dadi

cri

Kwanan baya rundunar sojojin kiyaye zaman lafiya ta rukuni na 3 da kasar Sin ta tura zuwa jihar Wau ta kammala aikinta kuma ta dawo nan kasar Sin bayan da ta shafe watanni 9 tana aikin kiyaye zaman lafiya a can. Lokacin da wadannan sojoji suke waiwaye kan zaman kiyaye zaman lafiya da suka yi cikin ranaiku fiye da 200, suna jin cewa, da akwai wahaloli da hatsarurruka, amma kuma da akwai abubuwa masu farin ciki da tafin hannu.

Kowace rana da asuba, akan busa kafon tashin barci, a lokacin kuwa akan ji koke-koken karnuka na daji, nan ne wani wurin da ke kudancin kasar Sudan wadda ta sha jurewar yakin basasa da aka yi cikin shekaru da yawa, a nan kura takan tashi ko'ina, kuma da akwai sauro da kwari masu dafi da yawa, shi ya sa akan kamu da cututtuka masu yaduwa. Amma a wannan wuri ne sojoji 435 na kasar Sin ciki har da sojoji injuiniyoyi da na masu yin sufuri da kuma masu aikin jiyya sun kago abin al'ajabi daya bayan daya. Lokacin da Mr. Zhang Yong, kwamisan siyasa na tabo magana kan wannan batu ya ce, "Mu ne wata rundunar kiyaye zaman lafiya wadda ta shafe lokaci mai tsawo domin tafiyar da aikinmu a nan, kuma daga cikin sojojin kiyaye zaman lafiya da suka samu yabo daga wajen kungiyar musamman ta MDD dake kasar Sudan, kuma ta zama rundunar kiyaye zaman lafiya daya kawai wadda ta samu yabo daga wajen kungiyar musamman ta MDD a gun bikin masu aikin jiyya, sa'an nan kuma ta kago al'ajabi cikin tarihin kiyaye laman lafiya wajen aikin likitanci, kuma ta sha juriya wajen karacin kayayyaki da matsalolin da suka faru ba zato ba tsammani."


1 2 3 4