Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-06-05 10:45:45    
Wata kungiyar masu aikin jinya ta kasar Rasha a lardin Sichuan wanda ke fama da mummunan bala'in girgizar kasa

cri

A wajen bikin ban kwana, a madadin gwamnatin birnin Pengzhou da jama'arta da yawansu ya kai dubu 780, magajin garin Pengzhou Mr. Han Yi ya nuna sahihiyar godiya ga kungiyar masu aikin jinya ta Rasha. Ya ce:

"Yayin da mummunan bala'in girgizar kasa ke fadawa lardin Sichuan, kungiyar masu aikin jinya ta Rasha sun zo nan birnin Pengzhou daga can nesa ba kusa ba. Da yake sharadin zamansu a nan ba shi da kyau, likitocin Rasha sun haye wahalhalu da dama domin yi wa mutanen da suka ji rauni sama da 1500 jiyya. Wannan al'amari ya bayyana irin kyakkyawar halayyar likitocin Rasha ta jin-kai, da dankon zumuncin a tsakanin jama'ar Sin da Rasha. Kazalika kuma, ya alamanta cewar, kyakkyawar dangantakar abokantaka bisa manyan tsare-tsare dake kasancewa tsakanin kasashen biyu ya kai wani sabon matsayi."

A gun bikin ban kwana, gwamnatin birnin Pengzhou ta mikawa kungiyar masu aikin jinya ta Rasha wata tutar nuna yabo, inda aka rubuta cewa "ceton mutane da tallafawa wadanda suka ji rauni" cikin harsunan Sinanci da Rashanci. Jami'an gwamnatin Pengzhou sun bayar da 'yan tsana na Panda a matsayin tsaraba ga kowane likita daga wannan kungiya.

Mataimakin shugaban kungiyar masu aikin jinya ta Rasha Mr. Ivanius Alexander ya ce, membobin kungiyar sun kafa kyakkyawar dangantakar abokantaka tare da jama'ar kasar Sin a cikin kwanaki sama da 10. Ya yi imanin cewar, ko shakka babu jama'ar kasar Sin za su iya hada kansu domin haye wahalhalu da sake farfado da matsugunnansu cikin gaggawa. Ivanius ya ce:

"Kowa ya sani, duk wata kasa da jama'arta ba za su iya kaucewa daga irin wannan bala'i daga Indallahi ba. Muddin dai mun hada kanmu, za mu iya rage irin hasarar da mummnunan bala'in ya janyo. Muna tare da ku har abada!"


1 2 3 4