Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-06-05 10:45:45    
Wata kungiyar masu aikin jinya ta kasar Rasha a lardin Sichuan wanda ke fama da mummunan bala'in girgizar kasa

cri

He Huawei, yaro ne mai shekaru 11 da haihuwa, wanda ya samu mummunan rauni a kafarsa ta hagu da kansa, a sanadiyyar mummunan bala'in girgizar kasa. Ya zauna a kan keken hannu, a wani yunkurin nuna godiya ga likitocin Rasha wadanda suka yi masa tiyata. Ya ce:

"Kawu da inna daga Rasha, yanzu na sami sauki sosai. Zan yi muku ramuwa da kyakkyawan karatuna a nan gaba!"

Wata yarinya mai shekaru 10 da haihuwa mai suna Dong Yao ta rera wata waka domin bayyana abin dake zuciyarta na nuna godiya ga likitocin Rasha, ta rera cewar:

"Na gode maka kwarai da gaske, saboda ka ba ni cikakkiyar jaruntaka wajen zaman kaina a cikin duk rayuwata".


1 2 3 4