Ranar daya ga watan Yuni na kowace shekara, ranar yara ce ta kasa da kasa. Amma ranar 1 ga watan Yuni na wannan shekara na da ma'ana ta musamman ga yara na yankunan da bala'in girgizar kasa ya ritsa da su a lardin Sichuan na kasra Sin. A ranar, a birnin Pengzhou na lardin Sichuan, mun ji muryar wakoki daga yara, inda suka nuna matukar godiyarsu ga wata kungiyar masu aikin jinya ta kasar Rasha wadda ta kokarta wajen gudanar da ayyukan jinya har na tsawon kwanaki 11 ba tare da tsayawa ba.
Tun daga ranar 20 ga watan Mayu na shekarar da muke ciki, membobin kungiyar masu aikin jinya ta Rasha suka fara isa birnin Pengzhou daya bayan daya, wadanda suka kasance mutane masu aikin jinya na kasashen ketare na kashin farko da suka shiga cikin yankunan da bala'in girgizar kasa ya ritsa da su bayan da mummunar girgizar kasa ta fadawa gundumar Wenchuan ta lardin Sichuan a ranar 12 ga watan Mayu. Bayan da suka gudanar da ayyukan jinya ba ji ba gani har na tsawon kwanaki 11, suka koma gida a ranar 1 ga watan da muke ciki da dare.
Da maraicen ranar 1 ga wata, an yi gagarumin bikin ban kwana da kungiyar masu aikin jinya ta kasar Rasha a birnin Pengzhou.
1 2 3 4
|