Ban da wannan, Abba Mohammed daga Kano, tarayyar Nijeriya, ya rubuto mana da cewa, "A gaskiya ina mai matukar alhini game da girgizar kasar da akayi a kasar Sin.Ina yi muku jaje.Allah ya kiyaye aukuwar haka a nan gaba.Allah ya mayar da abin da aka rasa. Allah ya taimaki gwamnatin kasar Sin wajen iya biyan wadan da wannan bala'i ya aukawa."
To, madallah, masu sauraro, sabo da karancin lokaci, ba za mu iya karanta muku wasiku daga wajen masu sauraronmu duka ba. A gaskiya, wasikun sun burge mu kwarai da gaske, sun kuma sosa mana rai sosai da sosai, sun ba mu goyon baya da karfi da gwarin gwiwa, sun shaida mana cewa, "abin da ya taba hanci ido ya yi ruwa", jama'ar Sin da na Afirka 'yan uwa daya ne. Sabo da haka, muna musu godiya kwarai da gaske. Kamar yadda masu sauraronmu suka fada, Allah ya ji kan wadanda suka rasa rayukansu, wadanda suka samu rauni, ya ba su lafiya, wadanda abin bai shafa ba, ya kare su. Masu sauraro, yau da shekaru 32 da suka wuce, wata girgizar kasa mai tsanani ta lalata birnin Tangshan na kasar Sin, tare da hallaka jama'a masu yawan gaske, har zuwa yanzu, jama'ar kasar Sin ba su iya mantawa da wannan babbar masifa ba. Amma abin da ya burge jama'a shi ne birnin Tangshan da aka farfado da shi bisa kufayi, wanda yanzu ya kasance wani kyakkyawan birni na zamani. Sabo da haka, muna da imanin cewa, jama'ar da girgizar kasa ta galabaitar da su za su share hawaye, su fita daga mawuyacin hali, za su farfado da garinsu, za su sami makoma mai kyau.
To, jama'a masu sauraro, karshen amsoshin wasikunku ke nan daga nan sashen Hausa na rediyon kasar Sin, muna muku godiya da sauraronmu, kuma da haka, ni Lubabatu daga nan Beijing ke cewa, a kasance lafiya. (Lubabatu) 1 2 3 4
|