Jama'a masu sauraro, assalamu alaikum, barkanku da war haka, barkanmu da sake saduwa da ku a zaurenmu na Amsoshin Wasikunku, kuma ni ce Lubabatu ke gabatar muku da wannan shiri daga nan sashen Hausa na rediyon kasar Sin.
Masu sauraro, kamar yadda kuka sami labarin cewa, a ran 12 ga watan nan da muke ciki, girgizar kasa mai tsanani, wadda karfinta har ya kai digiri 8 bisa ma'aunin Richter, ta afka wa gundumar Wenchuan ta lardin Sichuan da ke kudu maso yammacin kasar Sin. Sakamakon girgizar kasar, dubu duban mutane sun riga mu gidan gaskiya, a yayin da mutane masu yawan gaske suka ji raunuka. Wannan bala'i na ba zata ya bakanta wa jama'ar kasar Sin rai kwarai da gaske, amma ba mu kawai ba, masu sauraronmu ma suna mai da hankalansu sosai a kan al'amarin, suna bakin ciki, kuma sun aiko mana dimbin wasiku da sakonni, don nuna mana jaje da kuma nuna alhini da ta'aziyya ga wadanda suka riga mu gidan gaskiya sakamakon girgizar kasar. To, masu sauraro, a cikin shirinmu na yau, bari mu kawo muku wasu daga cikin wasikunsu.
Bala Mohammed Mando daga Abuja, tarayyar Nijeriya, ya rubuto mana cewa, "na samu wannan mummunan labari ta shafinku na internet, kuma ina bin yadda abubuwa ke gudana. A gaskiya, na yi matukar bakin ciki kuma ina kara juyayin wannan abu da ya faru. Musamman ma sabo da ina sha'awar jihar Sichuan kwarai da gaske. Ra'ayina shi ne, a gaskiya, gwamnatin kasar Sin ta yi matukar rawar gani wajen kawo gudummawa cikin hanzari ga jama'ar da wannan bala'i ya fada wa, kuma duk duniya ta shaida yadda manyan jami'an gwamnati da sauran jama'ar kasar suka tashi tsaye wajen kai taimako. Wannan ya nuna cewa, gwamnatin kasar Sin tana da tanadi da kuma tsari mai kyau na kulawa da al'ummarta a duk lokacin da wani abu ya auku, kuma jama'ar kasar Sin sun nuna wa sauran duniya yadda kansu yake a hade, da kuma yadda suke kaunar junansu. Sabo da haka, ina kara taya ku bakin ciki da kuma fatan kar Allah ya kara kawo irin wannan abu da ya faru. Ina kuma rokon kasashen duniya da kungiyoyin taimaka ma al'umma su kai gudummawarsu ta gaggawa ga jama'ar da wannan abu ya shafa."
1 2 3 4
|