Sai kuma shugaba Mohammed Idi Gargajiga daga Gombawa CRI listeners Club, jihar Gombe tarayyar Nijeriya, ya rubuto mana cewa, "A madadin dukkan masu sauraro na kungiyar gombawa cri listeners club da ni kaina shugaban club, muna taya gwamnatin kasar Sin tare kuma da iyalan wadanda suka rasa rayukansu da wadanda suka samu rauni da sauran jama'ar kasar Sin baki daya bakin ciki da juyayi tare da nuna alhini dangane da aukuwar mummunar girgizar kasa na gundumar Wenchuan ta jihar Sichuan ta kasar Sin. Muna kira ga dukkan jama'ar kasar Sin da su yi hakuri su dauki wannan lamari kaddara ne daga indallahi, kuma Allah zai maida gurbinta da alheri, kuma muna fata jama'ar kasar Sin baki daya su sa babban kokari wajen kawar da barnar da bala'in ya haifar cikin gaggawa, san nan kuma kasar Sin tana da nasara kuma za ta yi nasara a gasar wasannin olympic ta Beijing 2008."
Sai kuma daga birnin Yamai, jamhuriyar Nijer, malam Mamane Ada, ya turo mana wasikar da ke cewa, "Na aiko wannan sako zuwa ga masu sauraren cri, don nuna cewa hakika abunda ya taba hanci ido ruwa, shi ke ma'ana abun da ya taba kasar Sin ya taba mu, abunda ya auku ranar 12 ga wannan wata a gundumar Wenchuan ta jihar Sichuan dake yammacin kasar Sin cewa da girgizar kasa mai karfin digiri 7,8 na ma'aunin Richter, bala'in da ya haddasa mutuwar mutane kusan dubu goma tare da raunana mutane dimbin bayan kuma asarar dukiya da kadarori masu yawan gaske. Na ji matukar bakin ciki da bacin rai kan wannan al'amari, don haka ina aika ta'aziyyata ga iyalan mamatan. Allah kuma ya ji kansu, ya ba kuma danginsu hakurin zama. Daga karshe ina kira ga kasashen duniya da su tashi tsaye domin taya kasar Sin zaman makoki; sanan kuma su taimaka wajen kamama Sin shirya wasannin olympics na Beijing 2OO8, yin haka zai kawo ragowar bacin rai ga sinawa,fatana na karshe shine kadda irin wannan ya sake abkuwa kasar Sin da ma sauren kasashe na duniya sanan kuma ya kare mutanen wannan yanki daga sauren wasu bala'o'i.AMEN"
Akwai kuma Salisu Mohammed Dawanau, mai sauraronmu daga Abuja, tarayyar Nijeriya, wanda ya rubuto mana cewa, "jiya da rana na karanta wannan mummunar labari mai tausayawa ainun, ko mutun bai da dan'uwa idan ya samu labarin hadari, komai kankantarsa, to dole ne mutum ya nuna tausayawa da kuma yin jaje ga 'yan uwa da kuma mutanen da abin ya shafa.A gaskiya, wannan girgizar kasa da ya faru a gundumar Wenchuan ta jihar Sichuan abin jajantawa ne da kuma ban tausayi. Ina fata Allah Ya jikan wadanda suka rasa rayukansu, ina fata 'yan uwansu za su yi juriya sosai game da rashinsu, kuma ina fata wadanda suka yi rashin muhalli su ma su sami agaji cikin gaggawa.Bayan haka, ina taya duk wadanda abin ya shafa yin addu'a domin kada a sake samun kwatankwacin wannan mummunar al'amari. Kuma a sashen Hausa, ina taya ku bakin ciki sosai game da abinda ya faru."
1 2 3 4
|