Bayan haka, shugaba Abdullahi Baji daga Mobaji Radio Club, Kano, Nijeriya, ya rubuto mana cewa, "mun samu labarin girgizar kasa a kasar Sin, mun yi bakin ciki da jimami bisa wannan mummunan labari da ya faru. Sabo da haka, mu 'yan kungiyar Mobaji Radio Club muna mika ta'aziyyarmu gare ku dangane da wadanda suka rasu. Ga wadanda suka ji rauni, muna fatan Allah ya ba su lafiya."
Ga kuma sako daga hannun Shuaibu Muhammed Rijiyar Maikabi, daga Karamar Hukumar Kamba,Jihar kebbi, tarayyar Nijeriya. Ya ce, "dalilin rubuto muku wannan wasika shi ne In jajinta ma al'ummar kasar China da gwamnatin kasar Sin, Ba ma kasar Sin ba, al'ummar kasashen duniya suna juyayin wannan hadarin, bala'in girgizar kasar Sin Wallahi Ya mai da hankalin duniya wuri daya, don kasar Sin kasa ce wadda take taimakawa duk kasar da ta samu kanta cikin irin haka ko kwatan kwacin hakan, Allah ya Ji kan Wadanda suka rasa rayukansu, sannan Wadanda suka samu rauni, Allah ya ba su lafiya, wajen wadanda abin bai shafa ba Allah ya kare su."
Sai kuma Aliyu Yahuza daga Hammaruwa Way,Jalingo, jihar Yaraba, ya rubuto mana cewa, "dalilin wannan wasikar itace in mika ta'azi yata ga mutanen Sin baki dayan su a game da mutane masu yawa da suka riga mu gidan gaskiya. Ga wadanda suka samu rauni kuma, Allah ya sauwake, ga wadanda ba abin da ya same su kuma. Allah ya kara kiyay wa."
1 2 3 4
|