Torcilan abu ne da ke daukar wutar wasannin Olympics, kuma a wasannin Olympics na kowane karo, a kan fitar da wani sabon torcilan da ya dace da fasahar zamani, wato dole ne ya tabbatar da wutar da ake mikawa ba za ta mutu ba, sa'an nan, ya iya jure duk wani mummunan yanayi, kamar iska mai karfi da ruwan sama da dusar kankara da dai sauransu. Torcilan ya kan zama kayan tarihi na wasannin Olympics.
Sa'an nan, a game da tarihin babbar mai jagora ko babbar fada a bikin kunna wutar wasannin Olympics na Beijing, Maria Nafpliotou, wadda ta kasance babbar fada ta 10 a bikin tun daga shekarar 1936. An haife ta ne a birnin Athens, kuma tun lokacin da take karama, tana son rawa sosai, haka kuma ta nuna gwaninta sosai a wajen rawa. Daga baya, ta koyi rawa a wata makarantar koyar da rawa ta kasar Girika. Ita malama Maria Nafpliotou wani mai rawa ce mai cin nasara, haka kuma 'yar wasan kwaikwayo ce da ke samun yabo sosai daga masu kallo.(Lubabatu) 1 2 3 4
|