Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-03-28 12:44:28    
Wutar wasannin Olympics na Beijing

cri

A kan kunna wutar wasannin Olympics ne a gaban fadar Hera da ke garin Olympia, wato asalin wurin da aka fara yin wasannin Olympics, kuma a wasu watanni kafin a gudanar da wasannin Olympics. Sa'an nan, a kan bi hanyar gargajiyar Girika wajen kunna wutar, wato da farko, babbar fada a wurin ibada za ta karanta kasidu domin Appolo a gaban fadar Hera, sa'an nan, babbar fada za ta kunna wutar bisa wani madubi, wannan kuma hanya ce kawai da za a bi wajen kunna wutar wasannin Olympics. Sa'an nan, babbar fada za ta sanya wutar a cikin wani kwano, kuma da wutar ne za ta kunna torchilan da ke hannun mai mika wutar. Daga nan kuma, aka fara mika wutar wasannin Olympics, kuma wutar ta kama hanyar zuwa birnin da zai karbi bakuncin gudanar da wasannin Olympics.

Masu mika wutar wasannin Olympics mazanni ne da ke yada manufar wasannin Olympics. Kullum hukumar kula da wasannin Olympics ta duniya na ba da shawarar cewa, kamata ya yi jama'a su ne su mika wutar yola ta wasannin Olympics, wato jama'a duk wanda ke iya rike da torcilan tare da kammala gudu cikin zangon da aka kayyade, to, yana da damar zama mai mika wutar yola ta wasannin Olympics.


1 2 3 4