Tambayar da za mu amsa a wannan mako ta fito ne daga hannun malam Idris Adamu, mazaunin garin Funtua, jihar Katsina, tarayyar Nijeriya. A cikin wasikar da ka turo mana, ka ce, na ji kun ce, an kunna wutar wasannin Olympics na Beijing, shi ya sa ina so a ba ni karin bayani dangane wutar. Shin yaushe ne aka fara wannan biki na kunna wutar, yaya ake zaben wadanda za su mika wutar da makamantansu. Sa'an nan, a ba ni tarihin babbar jagora a bikin kunna wutar, wato Maria Nafpliotou.
A ranar 24 ga watan nan da muke ciki a birnin Olympia na kasar Girika, an kunna wutar wasannin Olympics da za a gudanar a birnin Beijing, sa'an nan, an fara mika wutar. Ita wutar wasannin Olympics wuta ce da aka kunna a garin Olympia na kasar Girika, bisa amincewar hukumar kula da wasannin Olympics ta duniya. Ita alama ce ta manufar wasannin Olympics, wadda kuma ke alamantar fata da buri, haske da farin ciki, tare kuma da zumunci da zaman lafiya da zaman daidaici.
1 2 3 4
|