Akwai ka'idoji da dama game da mika wutar yola, kuma muhimman ka'idoji sun hada da "wuta daya, hanya daya da kuma biki daya", wanda ya bayyana huldar da ke tsakanin wasannin Olympics na zamani da na gargajiya. Wato a duk lokacin da ake mika wutar yola ta wasannin Olympics, ana mika wutar da aka samo daga garin Olympia ne kawai, kuma ba za a iya hada wutar da sauran wuta ba. sa'an nan, ana iya gudanar da biki daya kawai na mika wutar yola ta wasannin Olympics. An dai cimma wadannan ka'idojin ne bisa yarjejeniyar da hukumar kula da wasannin Olympics ta duniya da gwamnatin Girika suka kulla, har ma ka'idojin sun zama al'adu wajen mika wutar yola ta wasannin Olympics.
Bayan haka, hukumar kula da wasannin Olympics ta duniya ita ce ta kan tabbatar da yawan masu mika wutar yola da birane da kasashen da za a bi wajen mika wutar da dai sauransu.
A lokacin da mai mika wutar yola na karshe ya shiga babban filin wasannin Olympics, kuma ya kunna wuta a filin, to, an fara wasannin Olympics ke nan.
1 2 3 4
|