Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-02-26 08:49:31    
Bayani kan yadda Sinawa ke gudanar da bikin sabuwar shekara tasu

cri

B : Zamani ya canza,zaman rayuwarsu ma na kara inganta. A halin yanzu mutanen da suke kaiwa juna ziyara su kan kasance ne dauke da abubuwa na zamani kamar su taba da giya mafi ingancin da suka fi shahara. A cikin shekarun baya bayan, kawo abubuwan gina jiki ya zama wani sabon yayi sa'ad da ake bayar da kyaututtuka a bikin yanayin bazara. Wani sa'i ma akan aika da wani kati na binciken lafiyar jiki ga aminai da abokansa domin nuna fatan alheri na sabuwar shekara da kuma fatan koshin lafiya, wannan salon da aka bi ya kara samun karbuwa daga jama'a.

A : da aka shiga rana ta biyar ta sabuwar shekara, mutanen kasar Sin su kan ci abincin da ake kira jiaozi cikin sinanci, A tatsuniyar gargajiya ta kasar Sin an ce a rana ta biyar ta sabuwar shekara allolin kudi sukan kawo kudi da sa'a ga mutanen duniya. Sabili da haka mutanen duniya su kan shirya gaggarumin bikin maraba da zuwan allolin kudi. Da aka shiga sabon zamani,ba a gudanar da irin bikin maraba da zuwan allolin kudi ba maimakonsa a kan ci abincin Jiaozi.

B :kamanin abincin Jiaozi ya yi kamar taguwa,wata siffar kudi ce da aka yi amfani da shi a zamanin can can da a kasar Sin. Da aka shiga rana ta biyar ta sabuwar shekara, mutanen Sin su kan ci irin abinci,wannan yana nufin cewa za a samu karin kudi a sabuwar shekara. Ban da wannan kuma a kan sa wani abinci daban a cikin abincin Jiaozi, abincin da aka sanya cikin Jiiaozi yana da ma'anoni masu kyau da yawa domin fatan alheri na sabuwar shekara. Alal misali, a kan sa alewa a cikin Jiaozi, idan wani ya ci Jiaozi dauke da alewa, wannan yana alamta cewa zai sami zaman jin dadi a sabuwar shekara, wani sa'I ma aka sa kerarrin kudi (coins) a cikin Jiaozi, idan wani ya ci,to wannan yana nufin cewa mutumin nan zai samu kudi mai yawa a sabuwar shekara.

A: ranar 15 ga watan farko na sabuwar shekara,ranar biki ce ta fitilu. A wannan rana da dare, wata ta cika (moon is full). Da magariba, mutane su kan kwarara zuwa tituna suna kallon fitilu masu launi daban daban sun shiga wasan kacici kacici.

B: A wannan rana mutanen Sin su kan ci wani irin abincin da ake kira Yuanxiao, abinci ne da aka yi da garin shinkafa, siffarsa kamar wani karamin kwallo ne a kan sa abinci mai dadi a ciki. A kan dafa su ta hanyoyi daban daban. A harshen sinanci, lafazin kalmar Yuanxiao ya yi makamanci da kalmar haduwa. Mutanen Sin su kan ci abincin Yuanxiao ne domin bayyana fatansu na kasancewar haduwar iyali. Idan wani dan iyali bai komo ba sai sauran 'yan iyali suna begensa da yi masata fatan alheri.

An kai karshen bukukuwan murnar sabuwar shekara ta sinawa ne bayan da aka gudanar da bikin fitilu a ranar 15 ga watan farko bisa kalandar gargajiya na kasar Sin. Tare da ci gaban zamani da sauye sauyensa, an kuma kawo sauyi ga al'adu da dabiu ga bukukuwan da sinawa ke gudanar da su bisa al'ada, duk da haka burinsu na zaman jin dadi da fatan alheri bai canza ba.To wannan shi ya kawo karshen shirinmu na yau mun gode muku saboda kun saurarenmu.(Ali)


1 2 3 4