Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-02-26 08:49:31    
Bayani kan yadda Sinawa ke gudanar da bikin sabuwar shekara tasu

cri

A cikin shirinmu na yau za mu kawo muku wani bayani na musamman kan yadda mutanen kasar Sin suke gudanar da bikinsu na sabuwar shekara tasu.

B: Bisa kalandar gargajiya ta kasar Sin, ranar 7 ga watan Fabrairu, bikin yanayin bazara ne na al'adun gargajiya na kasar Sin. Ga mutanen kasar Sin, bikin yanayin bazara gaggarumin biki ne a duk shekara. Ana yin bukukuwa iri iri domin murnar bikin nan tun daga ranar farko zuwa ranar 15 ga wata. A lokacin da ake yin bukukuwa, ana yin tsofaffin wasanni iri iri na gargajiya masu ban sha'awa da yawa shekara da shekaru. Yanzu mu shere ku da wasu abubuwan masu ban sha'awa da aka yi yayin da ake gudanar da bikin yanayin bazara.

A :Bisa kalandar gargajiya ta kasar Sin, a ranar farko ta watan farko, mutanen Sin su kan mika gaisuwar fatan alheri ta sabuwar shekara. Da safe maza da mata tsofaffi da yara su kan sa kayan ado su kan tafi gidajen danginsu ko abokansu domin mika gaisuwar fatan alheri ta sabuwar shekara, wasu suna gida suna jiran zuwan baki. Da suka ga juna, su kan ce " barka da sabuwar shekara"ko"ina yi maka fatan alheri na sabuwar shekara."

B :Yayin da ake mika gaisuwar fatan alheri, yara da samari su kan nuna fatan alheri na sabuwar shekara ga manya da tsofaffi kuma suna fatan tsawon rai da zaman lafiya su tabbata gare su. Manya da tsofaffi su kan ba yaran da samarin kyaututtukan kudi.

A :A kan bayar da kyaututtukan kudi a jajibere ko ranar farko ta sabuwar shekara. Idan aka yi a jajibere ba za a maimaita shi a kashegari ba.


1 2 3 4