Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-02-26 08:49:31    
Bayani kan yadda Sinawa ke gudanar da bikin sabuwar shekara tasu

cri
 

B: Da ka sarrafa inji mai kwakwalwa wato computer a turance, wasan wuta ya fito fili, kana iya ganin yadda ake yin wasan, kuma kana jin kara iri iri kamar ka sami kanka a ainihin halin yin wasan.

A: a rana ta biyu ta sabuwar shekara, mutane tsofaffi da yara su kan ziyarci dakunan ibada inda aka yi gangami. Inda aka shirya wasannin gargajiya na dabi'u da al'adun kasar Sin daban daban sai ka ce bikin kanival ne na kasar Sin, da akwai masu sayar da abinci iri iri masu dadin ci, da kuma kayayyakin wasa da kuma abubuwan kallo, mutanen suna kai da kawowa a harabar dakin ibada suna gudanar da bikinsu cikin halin nishadi da farin ciki.

B. A wuraren dake akwai dakunan ibada ,mutanen Sin su kan yi gangami a ranakun biki,suna gudanar da wasanni iri iri na gargajiya, kamar su wasan fitilu masu sifar dodanni da raye raye na zakoki da wasan hawan sanduna da dai sauransu.

B: wasan hawan sanduna yana da ban sha'awa kwarai da gaske. Mai yin wasa ya kan shiga burtun mashahuran mutane na tarihi, da ya ke an daura sanduna masu tsawo kan kafafuwansa, yana tafiya a kan sanduna, duk da haka yana tafiya yadda ya ga dama kamar a kasa yake tafiya, yana rawa kuma yana tsalle da jujjuyawa.

A: Jama'a masu sauraro,wakar da kuka ji waka ce mai suna "matan aure ta ziyarci gidan iyayenta. " A wannan rana,wato rana ta biyu ta sabuwar shekara, wajibi ne matan aure ta koma gidan iyayenta. Bisa al'ada da ake bi shekara da shekaru a kasar Sin, dole ne mata na zama tare da mijinta bayan ta yi aure, ba ta da dama da yawa da ta kai ziyara a gidan mahaifinta. Shi ya sa a rana ta biyu ta sabuwar shekara, matan da ta yi aure ta ziyarci gidan iyayenta, ta hadu da iyalin iyayenta, ta haka kuwa za a kara dankon zumuncin da ke tsakanin iyalai biyu da ke da alakar aure. A wannan rana, iyayen matan aure su kan shirya abinci iri iri masu dadin ci ga diyarsu da surukinsu, su kan yi hira cikin halin annashuwa da kwanciyar hankali, iyayen matan aure kuma sun iya samu labarai kan yadda diyarsu ta yi zama a gidan mijinta.

B : Ba safai a kan yi haduwa ba, shi ya sa lokacin da matan aure ta ziyarci gidan iyayenta, ta kan kawo wasu kyaututtuka domin iyayenta da kuma 'yan uwanta. Wakar da kuka ji dazu waka ce da ta siffanta irin wannan halin da ake ciki. Wakar ta yi nuni da cewa "dauke da kaza daya a hannun hagu da agwagwa daya a hannun dama, tana kawo wani jariri mai kiba a bayanta."wannan waka ta siffanta yadda matan aure ta ziyarci gidan mahaifinta a rana ta biyu ta sabuwar shekara. "

A : Da aka shiga rana ta uku ta sabuwar shekara, mutane kan kai wa juna ziyara. A wannan rana aminai da dangi da kuma abokai masu arziki su kan kai wa juna ziyara dauke da kyaututtuka. Suna yi wa juna fatan alheri da kara dankon aminci ta hanyar nan. A da mutane na kai wa juna ziyara dauke da kanana akwatunan da ke kunshe da abubuwa masu dadin ci da zummar kara karfin zumuncin dake tsakaninsu.


1 2 3 4