Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-02-26 08:49:31    
Bayani kan yadda Sinawa ke gudanar da bikin sabuwar shekara tasu

cri

B: gaskiyarka. A da kudin kyauta da aka baiwa yara da samari bai yi yawa ba, yaran da samarin da suka samu kyaututtukan kudi su kan yi amfani da su wajen sayen abin lashe-lashe da tande-tande ko kayan wasa. Ga shi a yau zaman sinawa na kara kyautattuwa, kudin kyautar da aka baiwa yara da samari ya kara yawa, wasun yaran sun tattara kudaden da aka ba su, sun maida su kudin taimako, sukan aika da kudin zuwa ga takwarorinsu 'yan makaranta da ke zama a cikin yankin duwatsu da ke fama da talauci a ganinsu hakan ke da muhimmiyar ma'ana.

A: karar da kuka ji kara ne da akan ji a yayin da ake yin wasan wuta. Wasan wuta wani muhimmin wasa ne da ake yi daga cikin wasannin gargajiya masu ban sha'awa da ake yi a ranar farko ta sabuwar shekara. An ce karar wasan wuta tana kore abubuwa masu bata rai da marasa kyau daga zukatan jama'a da kuma kawo farin ciki da fatan alheri da kuma abubuwa masu kyau a gida.

B: Tare da ci gaban zamantakewa da karin wayen kai na mutanen kasar Sin kan kiyaye muhalli. Tun daga shekara ta 2005 an kayyade wasan wuta a yankuna biyar da ke cikin birnin a wasu wurare cikin wasu lokuta. Mazaunan birnin Beijing ba su yi wasan wuta yadda suka ga dama kamar yadda suka yi a da ba duk domin kiyaye muhallin birnin Beijing. Duk da haka ba za su iya mantawa da wasan wuta mai ban sha'awa ba.

A: Ga shi yanzu wasu tasoshi na yanar gizo ta internet sun fitar da shirye-shiryen wasan wuta a shafunansu duk domin shere mazaunan birnin da wasan wuta.


1 2 3 4