
Mataimakin shugaba Hu Wei na jihar Xinjiang ya yi hasashen cewa:
'Za mu mayar da aikin yawon shakatawa tamkar wata gada ce domin inganta zumuncin da ke tsakanin 'yan kabilun jiharmu da jama'ar kasashen waje da kuma sa kaimi kan amincewa da juna da hadin gwiwarsu. Cikin sahihanci ne muka gayyaci karin baki na ketare zuwa jihar Xinjiang domin kara fahimta kan al'adun tarihi na Xinjiang mai dogon tarihi da kyan karkara da kuma karfin jiharmu.'
Watan Yuli da na Agusta da na Satumba na ko wace shekara lokuta ne mafiya dacewa na kawo wa jihar Xinjiang ziyara. Tabbas ne ire-iren danyun 'ya'yan itatuwa masu rahusa za su cancance ku.( Tasallah) 1 2 3 4
|