
In an tabo magana kan jihar Xinjiang ta Uygur mai ci gashin kanta da ke arewa maso yammacin kasar Sin, a kan tuna da 'yan kananan kabilu da ke da budaddiyar zuciya da kuma kide-kiden kabilu masu sigar musamman. Amma yau za mu ziyarci wurin tarihi na garin Kuche mai dogon tarihi.
Ma'anar Kuche a bakin 'yan kabilar Uygur ita ce mai dogon tarihi. A can da, mutanen Sin sun kira shi 'Qiuzi'. Kuche na kasancewa a tsakiyar kudancin manyan tsaunukan Tianshan, kuma a bakin iyakar kwarin Talimu a arewa a jihar Xinjiang, shi ne kuma mafari na al'adun Qiuzi. Malam Ma Xingtian da ya zo daga yankunan tsakiyar kasar Sin ya kai wa Kuche ziyara a karo na farko, ya bayyana cewa:
'A ganina, wuraren da ke jihar Xinjiang na da kyan gani ainun. Kyan karkara a wajen sun sha bamban da na sauran wurare. Sun karfafa gwiwar mu da kuma ba mu mamaki sosai. Mun yi zumudi sosai domin ganin kyan karkara masu ban mamaki.'
1 2 3 4
|