Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-11-27 16:35:30    
Wurin tarihi na tsohon garin Kuche da ke jihar Xinjiang ta Uygur mai ci gashin kanta ta kasar Sin

cri

A watan Yuli na wannan shekara, an bude bikin harkokin yawon shakatawa na kasa da kasa na jihar Xinjiang a karo na 4 da kuma bikin harkokin yawon shakatawa da al'adun Qiuzi na Kuche.'Yan kasuwa na cinikin yawon shakatawa fiye da dubu guda da suka zo daga kasashe da yankuna 22 na duniya da mazaunan wurin na kabilu daban daban sun kara fahimtarsu kan kyakkyawan al'adun Qiuzi tare. Da zarar suka sauka daga jirgin sama, sai al'adu da kyaun karkara na wurin su burge su sosai, bi da bi ne suka bayyana cewa, jihar Xinjiang wuri ne da aka fi samun albarkatun yawon shakatawa a kasar Sin, tana da babban karfin da ba a taba amfani da shi ba tukuna, tabbas ne za ta jawo hankulan kasashen duniya a fannin harkokin yawon shakatawa a nan gaba.

In masu yawon shakatawa da suka zo daga sauran wurare suna kawo wa Kuche ziyara, da farko dai su kan more bakinsu da danyun 'ya'yan itatuwa da abinci iri daban daban da ke bayyana sigogin musamman na kananan kabilun kasar Sin. A ciki kuma, naman dan tunkiya ya fi yin suna. A ko wace rana da safe, kamshin da naman dan tunkiya ke samarwa a lokacin da mazaunan wurin 'yan kabilar Uygur suka gasa shi ya cika tituna, har ma mutane kan ji yunwa.

Bugu da kari kuma, raye-raye irin na Qiuzi da ke bazuwa a Kuche ya dade ya shahara, haka kuma, yana da dogon tarihi. Shi ya sa, an mayar da Kuche garin raye-raye da wake-wake. Raye-raye irin na Qiuzi ya taba bazuwa da kuma ba da tasiri a kasashen Japan da Korea ta Arewa da Persia da Viet Nam da Indiya da Larabawa da arewacin Afirka. Sa'an nan kuma, ya taba ba da babban tasirinsa kan wadatuwa da bunkasuwar kide-kide da raye-raye da wasannin kwaikwayo da kuma wasan acrobatics na kasar Sin.


1 2 3 4