Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-11-27 16:35:30    
Wurin tarihi na tsohon garin Kuche da ke jihar Xinjiang ta Uygur mai ci gashin kanta ta kasar Sin

cri

Kuche na bangaren tsakiya na tsohuwar hanyar siliki ta kasar Sin, shi ne wurin da al'adun yankin tsakiya da yankin yamma na kasar Sin suka hadu da juna. An iya kara fahimta kan addinin Buddha mai tsawon shekaru dubu 2 da kuma ganin zane-zanen jikin bango da aka saka a cikin kogunan dutse mafiya girma da yawa da ke yamma da yankin Dunhuang da kuma kallon raye-raye irin nan Qiuzi.

Kuche na matsayin daya daga cikin gundumomi da birane guda 4 mafiya shahara a jihar Xinjiang, inda aka samu yawan ramukan dutse da tsofaffin fadace-fadace da wuraren ba da gargadi kan zuwan abokan gaba da sauran wuraren tarihi fiye da 80, haka kuma, akwai ramukan dutse fiye da 500 da kuma znae-zanen jikin bango masu fadin murabba'in mita dubu 20.

Malam Teng Shaozhen, shugaban wani kamfanin yawon shakatawa, ya kawo wa Kuche ziyara daga kasar Australia. Yana ganin cewa, abun da jihar Xinjiang ke fi jawo hankulan masu yawon shakatawa shi ne al'adu masu dogon tarihi. Ya ce:

'Lalle akwai kyawawan wurare a wajen. Ina tsammanin cewa, ban da kyaun karkara, akwai dimbin abubuwan al'adu a jihar Xinjiang. Mutanen Sin kan yi alfahari domin yi wa kasashen duniya bayani kan tarihin kasarsu. Shi ya sa na dauki hotuna da yawa, zan gabatar da jihar Xinjiang ga baki. A zahiri suna sha'awar al'adun kasar Sin sosai. A ganina, jihar Xinjiang na fuskantar kyakkyawar makoma wajen raya aikin yawon shakatawa.'


1 2 3 4