Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-10-30 15:43:45    
Kyakkyawan yanayin rayuwa da al'adun kabilu a yanki mai dimbin duwatsu wato Shilin

cri

A cikin dogon tarihi, mazauna wurin da tsarin yanayin kasa na Karst na yankin Shilin da kuma duwatsun da suka fito da irin wannan tsarin yanayin kasa na musamman sun kulla kyakkyawan hulda a tsakaninsu, har ma ba za a iya raba su ba. Mutanen Sani na zamanin da sun yi sassaka da kuma zane-zane kan kusoshin duwatsun da ke yankin Shilin game da harkokin sadaukarwa masu dogon tarihi da raye-raye da farauta da yake-yake. Ma iya cewa, yankin Shilin na ba da babban tasiri kan rayuwar mutanen Sani daga dukkan fannoni, kamar su addini da almara da rubutattun wakoki da raye-raye da surfani da tufafi da gine-gine da bukukuwa da dai sauransu. Irin wannan kyakkyawan yanayin rayuwa da al'adun kananan kabilu kan burge masu yawon shakatawa na kasashen waje da ke ziyara a yankin Shilin. Madam Briana Lopez, 'yar kasar Australia, ta ce,

'Mun nuna sha'awa sosai kan wannan. Kananan kabilu da yawa na zama a wurin. Gano tarihinsu da kuma al'adunsu shi ne wani abu mai ban sha'awa.'

Yanzu karni da yawa sun wuce, almara game da Ashima ta kasance wani bangare ne na zaman rayuwar yau da kullum na mutanen Sani da bukukuwan aure da jana'iza da sauran al'adun gargajiya, tana ta bazuwa a tsakanin mutanen Sani.(Tasallah)


1 2 3 4