
A cikin shirinmu na yau, da farko dai, za mu dan tabo magana kan kyakkyawan yanayin rayuwa da al'adun kabilu a yanki mai dimbin duwatsu wato Shilin da ke lardin Yunnan, daga bisani kuma, za mu gabatar muku da bayanin wani fili ko kuma dakin wasa na taron wasannin Olympic na Beijing.
A yanki mai dimbin duwatsu wato Shilin da ke lardin Yunnan na kasar Sin, an tsugunar da mutane na wani reshen karamar kabilar Yi ta kasar Sin wato mutanen Sani, wadanda suka samar da al'adu game da 'Ashima' a yankin Shilin da kuma nagartattun kide-kide da wake-wake da raye-raye na kabilarsu. Yau ma bari mu matsa musu don kara fahimtar yanayin rayuwarsu da al'adun kabilarsu.
1 2 3 4
|