Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-10-30 15:43:45    
Kyakkyawan yanayin rayuwa da al'adun kabilu a yanki mai dimbin duwatsu wato Shilin

cri

A wurin yawon shakatawa mai suna Xiaoshilin da ke yankin Shilin, akwai wani tabki mai tsabtataccen ruwa, a bakinsa kuma, ya kasance da wani dutse, siffarsa ta yi kama da wata budurwa ta kabilar Sani. A kowace rana, dimbin masu yawon shakatawa na zuwa kallonsa da kuma daukar hoto. Malama Bi Yunhua, mai jagorantar masu yawon shakatawa ta gaya mana cewa, shi ne kusan dutse na budurwa mai suna 'Ashima'. Ana kiran dukkan budare mazauna wurin 'Ashima'. Ta ce,

'Mu kan kira budare na wurin da sunan 'Ashima'. Ma'anar 'Ashima' a bakin 'yan kabilar Yi ita ce budurwa mai kyan gani. Maza kuwa mu kan kira su 'Aheige', wato namiji mai aiki tukuru da kuma jaruntaka.'

Game da asalin kusan dutsen Ashima, akwai wata almara da ke da farin jini ga mazauna wurin. An haifi wata kyakkyawar budurwa a wani iyalin talakawa, iyayenta sun kira ta 'Ashima'. Ashima ta kware wajen rera waka da kuma yin raye-raye, matasa maza da yawa na kaunarta sosai. Ta shiga soyayya da wani maraya wai shi Ahei, ta yi alkawarin cewa, ba za ta auri saura ba sai shi kawai. A wata shekara, a gun bikin mika tocilan, Ahei da ita sun daddale yarjejeniyar aure. Amma wani dan mai kudi yana kaunar Ashima, har ya nemi aurenta. A wani lokaci ya kan yi mata barazana ko kuma ya yi mata babbar kyauta, amma duk da haka ya sha kaye, ya rasa abin da zai yi. Shi ya sa a lokacin da Ahei ya je wuri mai nisa domin kiwon raguna, mai kudi ya kwace Ashima, ya tilasta ta auri dansa, amma Ashima ta ki. Da jin wannan labari, Ahei ya yi rana da dare yana dawowa gida ya kubutad da Ashima. Mai kudi ya yi matukar fushi, a yayin da Ashima da Ahei suka ketare kogi, mai kudi ya sa ambaliyar ruwa ta wuce da Ashima. Bayan da wata mala'ika ta cece ta, Ashima ta zama kusan dutse.


1 2 3 4