Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-10-30 15:43:45    
Kyakkyawan yanayin rayuwa da al'adun kabilu a yanki mai dimbin duwatsu wato Shilin

cri

Mutanen Sani na kabilar Yi sun dade da zama a yankin Shilin daga zuriya zuwa zuriya. Galibin gidajen wurin da suka gina da duwatsu ta hanyar gargajiya. A daruruwan shekaru da suka wuce, kauyawa sun yi amfani da duwatsun da suka samu a wurin domin gina gidaje da shimfida hanyoyi. Malam Huang Xing, wanda ke nazarin al'adun gargajiya cikin dogon lokaci a wurin, ya gaya mana cewa, al'adun duwatsu da ke bazuwa a yankin Shilin na da dogon tarihi. Ya ce,

'Saboda kakanninmu sun yi shekara da shekaru suna zaune da kuma yin aikin kawo albarka a wannan yanki mai tsarin yanayin kasa na Karst, shi ya sa yau fiye da shekaru dubu 800 da suka wuce, sun san yadda suka yi amfani da duwatsu domin yaki da muhalli, sa'an nan kuma, sun fito da al'adun da ke da nasaba da duwatsu. Alal misali, akwai wasu kayayyakin dutsen da suka yi amfani da su a zamanin da, da kuma wasu kayayyakin masarufi da na aikin kawo albarka da suke amfani a yanzu.'


1 2 3 4