Koyon da nake yi daga malamina Qi Baishi na da halayen musamman sosai, na yi karatu a sashen koyar da fasahar yin zane-zane na jami'ar Furen, a sa'I daya kuma na koyi fasahar zane-zane daga malamina Qi Baishi, dangantakar da ke tsakanina da malamina Qi Baishi tana kasancewa tamkar yadda huldar da ke tsakanin mahaifi da dansa take yi. Babban abin da ya burge ni sosai shi ne, lokacin da na yi kuskure wajen yin zane-zane, sai malamina ya kai suka sosai gare ni, wannan ya nuna bambanci sosai a tsakanina da sauran dalibai, alal misali, lokacin da nake son yin zane-zane dangane da kifaye, ina tammanin cewa, abin da na zana ya yi tamkar sifar kifi kawai, amma malamina ya gaya mini cewa, ya kamata na mai da hankali sosai wajen duddubawa, ya ce, in ban duba sosai ba, to tabban ne ba zan sami ci gaba ba.
Mr Lou Shibai ya koyi fasahar yin zane-zane wajen Qi Baishi har da shekaru masu yawa, wajen yi zane-zane dangane da tsaunuka da kogi da tabki da teku da furanni da tsuntsaye da kifaye da kwari da rubuce-rubuce da wakoki, Mr Lou Shibai ya yi gadon fasahar malaminsa Qi Baishi sosai da sosai, hakan kuma ya yi gadon kirkinsa wajen yin zane-zane, an bayyana cewa, lokacin da aka yi kallon zane-zanen da Lou Shibai ya yi, ana kan samun kuskure da cewa, su ne zane-zanen da malami Qi Baishi ya yi. A lokacin Babban malami Qi Baishi ya ke da rai a duniya, ya taba cewa, ba ma kawai zane-zanen da Lou Shibai ya yi sun yi kama da nawa ba, hatta ma halinsa ya yi kama da nawa, nan gaba zai iya kara samun sakamako mai kyau sosai.
1 2 3 4
|