
Lokacin da sojojin Isra'ila suna tafiyar da matakan, sun gamu da kiyayya mai tsanani sosai da wasu mazauna suka yi, sun jefa kwan kaji da sauran kayayyaki, kuma wata mace soja ta ji rauni. Gama da adawar da mazauna suke yi, sojojin 'yan sanda na Isra'ila sun yi hakuri, amma ba su daina tafiyar da matakan. Kwamanda Uri Barlev na sojoin da ke kudancin Isra'ila ya ce, "Halin sojojin yana da wuya, suna shiga wuku, ina fata da karshe dai za a sani, dukanmu muna bin kabila daya ce"
Kudurin da gwamnatin Isra'ila ke dauka ya sa yawancin mazaunan su karbi matakan. Har zuwa ran 17 da dare, cikin duk iyalan mazauan Yahudawa dubu 1.5 da ke zirin Gaza, akwai iyalai dubu daya sun riga sun janye jiki, kuma wasu sun bukatar 'yan sanda su ba musu lokaci don shirya, kuma za su janye da kansu. Yanzu gwamnatin Isra'ila ta riga ta kwantar da mazaunai fiye da 250 a yankin Nichalim. Mr.Eldar jami'i mai kula da wurin ya ce, "Yankin Nichalim daya da ke cikin yankunan mafi kyau na Isra'ila, yana kusa da birnin Tel Aviv da gabar tekun Rum, yana da zaman lafiya sosai. Ya kamata mazauna su canja ra'ayoyinsu don fuskantar da nan gaba."
1 2 3 4
|