
Ran 17 ga wata, sojojin 'yan sanda na Isra'ila fiye da dubu goma sun shiga matsugunai da ke zirin Gaza, don tafiyar da aikin janye jiki daga zirin Gaza da karfi. Ko da ya ke an gamu da kiyayya mai tsanani da mazaunan Yahudawa suka yi, ana tafiyar da matakan gashin kai bisa shiri. A sa'i daya kuma, wasu mazaunen Yahudawa wadanda suka janye a baya sun riga sun zauna a Isra'ila sun fara sabon zamansu. Yanzu bari mu saurari rahoton da 'yan jarida na Rediyon kasar Sin He Jinzhe da Liao Jibo suke yi a matsugunai da ke zirin Gaza.
Neveh Dekalim shi ne Matsugunai mafi girma na Yahudawa da ke zirin Gaza, an ce Neveh Dekalim cibiyar matsugunai, kuma mazauna da yawa da ke wurin suna kiyayyar da matakan janye jiki. Ran 17 an fara tafiyar da matakan a wurin.
1 2 3 4
|