Kwanan baya, hukumar kiwon lafiya ta duniya wato WHO ta ba da shawarar cewa, yin rayuwa ta hanyar da ta dace yana iya rage barazanar kamuwa da ciwon karancin basira, kamar cin abinci yadda ya kamata, motsa jiki lokaci-lokaci, daina shan taba da giya da tabbatar da kula da nauyi.
Takardar jagorar ta gabatar da wasu shawarwari kan yin rigakafin kamuwa da ciwon karancin basira. Alal misali, ta shawarci baligai su rika motsa jiki don yaki da raguwar karfin fahimta. Da babbar murya ta shawarci a daina shan taba. Sa’an nan ta ba da shawarar cin abincin da ya dace, alal misali, abinci irin na tekun Mediterranean, wato a kara cin ‘ya’yan itatuwa da kayayyakin lambu, kifi, albarkar teku, wake, dangin gyada da hatsi, da kuma yin amfani da man zaitun wajen dafa abinci. Har ila yau a guji shan giya.
Haka zalika, takardar jagorar ta shawarci baligai su mai da hankali wajen kula da nauyin jikinsu, don magance yin kiba, tare da sa ido kan barazanar da ciwon hawan jini, ciwon sukari, lalurar damuwa da dai sauransu suke kawo wa lafiyar mutane. Dukkan wadannan matakai suna taimakawa wajen rage barazanar kamuwa da ciwon karancin basira da kuma raguwar kaifin fahimta.
Abin da ya kamata a lura da shi shi ne, ko da yake sabuwar takadar jagorar tana ganin cewa, babu wasu shaidu da ke nuna cewa, raguwar yawan harkokin tuntubar bangarori daban daban na al'umma tana da nasaba da raguwar kaifin fahimta. Amma ta yi nuni da cewa, tuntubar bangarori daban daban na al’umma tana amfanawa koshin lafiyar jiki da ma tunani. Don haka ta karfafawa mutane gwiwar da su rika tuntubar wasu a matakai daban daban na zaman rayuwarsu.
Hukumar WHO ta karfafawa kasashen duniya gwiwa da su tsara manufofi da matakai na yaki da ciwon karancin basira, ciki had da horas da masu kulawa da masu fama da lalurar kaifin basira, saboda a yawancin lokuta, mambobin iyalai ne masu fama da wannan matsala. A kan bukace su da su gyara yadda suke rayuwa da kuma ayyukansu don kulawa da masu fama da ciwon yadda ya kamata.
Masu fama da ciwon karancin basira su kan yi fama da karancin tunani, fahimta, yin magana, gudanar da harkokin yau da kullum. Alkaluman hukumar WHO sun nuna cewa, yanzu akwai mutane miliyan 50 dake fama da wannan matsala a duk duniya, a cikinsu kuma kaso 60 daga cikin wannan adadi suna zaune ne a kasashe masu karanci da matsakaicin kudin shiga. An kiyasta cewa, nan da shekarar 2050, yawan masu fama da ciwon karancin basira zai kai miliyan 152 a duniya. (Tasallah Yuan)