Wata kungiyar manazartan kasa da kasa ta Australia ta gano cewa, ‘yan mata sun fi matasa maza fuskantar barazanar dake shafar lafiyar tunaninsu sakamakon amfani da kayayyakin laturoni na zamani na dogon lokaci.
Sabon binciken, wanda aka wallafa a mujallar kiwon lafiyar yara da matasa ta Lancet ya gano cewa, yanayin lafiyar yara ‘yan mata zai iya tabarbarewa, bayan sun shafe mintoci 75 a kowace rana suna kallon kayayyakin laturoni na zamani, yayin da hakan ka iya shafar lafiyar yara maza da kusan mintoci 105.
Asad Khan, mataimakin farfesa kan ilmin kiwon lafiya da taimakawa masu cututtuka samun sauki a jami’ar Queensland ya ce, binciken ya nazarci bayanan matasa fiye da 577,000 ‘yan shekaru 13 zuwa 15 daga kasashe 42. Nazarin ya gano cewa, babu matsala ga yanayin tunanin matasan cikin awa na farko na fara amfani da kayayyakin laturoni na zamani a kowace rana, amma a kan samu mummunar illa daga bisani.
Masanin ya kara da cewa, mai yiwuwa ne amfani da kayayyakin laturoni na zamani fiye da kima zai iya haifar da ciwon damuwa, da matsalar kiba, da tabarbarewar yanayin zaman rayuwa, da rashin iya cin abinci kamar yadda aka saba, da kuma raguwar yanayin lafiyar jiki da kwarewar fahimta, alal misali, gamuwa da matsalar mantuwa da rashin mai da hankali kan wani abu.
Masu nazarin sun yi amanna cewa, duk da rashin amfani da kayayyakin laturoni na zamani, ‘yan mata sun fi matasa maza sha’awar gudanar da harkoki a cikin daki, wanda hakan yake zama daya daga cikin dalilan da ka iya haifar musu da illa cikin sauki.
Khan ya yi bayani da cewa, bincikensu ya nuna cewa, kara motsa jiki yana da matukar tasiri kan kyautata lafiyar tunanin matasa. Hakan ya tabbatar da abin da galibin iyaye suka jima suna nuna shakku a kai.
A cewarsa kuma, "Muna bukatar daukar cikakkun matakai domin rage yawan lokutan da matasa ke batawa wajen kallon kayayyakin laturoni na zamani da kuma kara yawan lokacin motsa jiki."
To, mene ne hakikanin matakan da za a iya dauka? Madam Zhang Chuji, wata likita ce da ke aiki a asibitin Tiantan na Beijing ta yi mana karin bayani da cewa, motsa jiki na tsawon sa’a guda da kuma sa’o’i da ba su zarce biyu ba a kowace rana wajen kallon kayayyakin laturoni na zamani zai fi dacewa da kyautata lafiyar tunanin matasa.(Tasallah Yuan)