Taron shekara-shekara na hadaddiyar kungiyar ilmin ciwon zuciya ta Turai a shekarar 2020 ya kaddamar da wani sakamakon nazari da masu ilmin kimiyyar kasar Sin suka gudanar, inda aka nuna cewa, idan mutane sun yi barci isasshe a kowane dare, to, samun hutu ko yin barci na tsawon lokaci da bai kai mintuna 30 ba a rana, yana taimakawa wajen kiwon lafiyar zuciyarsu. Amma idan lokacin barci ya wuce awa daya, to, watakila zai kara barazanar mutuwa da kaso 30 cikin 100.
Masu nazari daga jami’ar ilmin likitancin ta Guangzhou na kasar Sin wadanda suka gudanar da nazarin sun yi nuni da cewa, a sassa masu dimbin yawa a duniya, mutane sun saba da yin barci da tsakar rana, lamarin da ake daukar sa a matsayin wata hanyar kiwon lafiya. Ana ganin cewa, yin barci a tsakar rana yana kyautata yin aiki. Nazarin da masu nazarin na kasar Sin suka yi ya kalubalanci ra’ayoyin da aka tsaya a kai a baya.
Bisa abubuwan shaida da aka samu, masu nazarin kasar Sin sun kimanta alakar da ke tsakanin yin barci da tsakar rana da mutuwa da kuma barazanar kamuwa da cututtukan zuciya da na magudanar jini, inda suka yi nazari kan masu aikin sa kai dubu 313 da 651, wadanda suka shiga cikin nazarce-nazarce fiye da 20 da suka yi a baya. A cikin wadannan masu aikin sa kai, wasu kaso 39 cikin dari ne suka saba da yin barci da tsakar rana.
Masu nazarin sun gano cewa, gwargwadon wadanda ba sa barci da tsakar rana, wadanda suke daukar awa daya ko fiye da haka suna barci a tsakar rana sun fi fuskantar barazanar mutuwa da kaso 30 cikin dari, kana kuma yiwuwar kamuwa da cututtukan zuciya da na magudanar jini ta karu da kaso 34 cikin dari. Idan an yi la’akari da yin barci da dare, to, a cikin wadanda suke daukar awoyi 6 ko fiye da haka a kowane dare suna barci, yin barci cikin dogon lokaci a tsakar rana kan kara musu barazanar mutuwa.
Yin barci na tsawon lokacin da bai kai awa daya ba a tsakar rana, ba zai kara barazanar kamuwa da cututtukan zuciya da na magudanar jini ba. Masu nazarin kasar Sin sun yi nuni da cewa, watakila yin barci na mintuna 30 zuwa 45 a tsakar rana yana iya kyautata lafiyar zukatan mutanen da ba su yi barci isasshe da dare ba.
Ko da yake ya zuwa yanzu ba a san hakikanin dalilin da ya sa yin barci da tsakar rana ya ke tasiri kan lafiyar mutane ba tukuna. Amma wasu nazarce-nazarce sun shaida cewa, akwai wata alaka a tsakanin yin barci cikin dogon lokaci da tsakar rana da illa ga lafiyar zukatan mutane da ma tsawon rayukansu. Haka kuma a cikin wasu nazarce-nazarce, an danganta yin barci da tsakar rana da ciwon hawan jini, ciwon sukari da yadda jikin dan Adam ba ya aiki yadda ya kamata.
Madam Zhang Chuji, wata likita ce da ke aiki a asibitin Tiantan na Beijing ta ba mu shawarar cewa, idan ana son yin barci a tsakar rana, to, ya fi dacewa a yi barci cikin awa daya. Amma idan wasu ba su saba da yin barci da tsakar rana ba, to, ba sa bukatar yin haka. (Tasallah Yuan)