Jami’ar The Chinese University of Hong Kong ta kasar Sin wato CUHK ta sanar a kwanan baya cewa, kwalejinta na ilmin likitanci ya gudanar da nazari na farko a duniya dangane da iyalan masu fama da matsalar tafiya yayin da suke barci wato su kan tashi su je wani wuri yayin da suke bacci, ba tare da sun sani ba, inda aka gano cewa, wadanda ke da dangantaka ta jini kai tsaye da masu fama da tafiya yayin barci, sun fi masu koshin lafiya fuskantar barazanar kamuwa da ciwon Parkinson's har sau 3 zuwa 6.
Jami’ar CUHK ta yi karin bayani da cewa, matsalar yin tafiya yayin barci, wani nau’in ciwon barci ne, wanda aka dauke shi a matsayin wata muhimmiyar alama kafin a kamu da ciwon Parkinson's. Wadanda ke fama da matsalar yin tafiya yayin barci ba sa sarrafa jijiyoyinsu yadda ya kamata yayin da suke barci, su kan nuna karfin kamar yadda suke yi cikin mafarki, alal misali, buguwa, mirginawa da ihu, wadanda su kan jikkata jikin mutane.
Masu nazarin daga jami’ar CUHK sun gayyaci mutane 102 masu fama da matsalar yin tafiya yayin barci da kuma masu koshin lafiya 89 da kuma dangoginsu na jini kai tsaye 791, ciki had da mahaifa, ‘yan uwa da ‘ya’yansu.
An gano cewa, yan uwa na jini kai tsaye, na masu fama da matsalar yin tafiya yayin barci sun fi fuskantar barazanar kamuwa da wannan matsala, wato ciwon Parkinson's da matsalar da ke shafar kwakwalwa, har ta shafar yanayin koyo da adana muhimman abubuwa, har sau 3 zuwa 6. Ban da haka kuma, duk da dangogin ba sa kamuwa da matsalar, amma sun fi fama da matsalar yin bahaya, da rashin daidaituwar jiki, wadanda alamu ne na koma bayan kwakwalwar mutane.
Masu nazarin sun yi bayani da cewa, bayan shekaru 5 zuwa 15, kaso 90 cikin dari na masu fama da matsalar yin tafiya yayin barci su kan yi fama da alamun ciwon Parkinson's ko sauran alamun koma bayan kwakwalwa.
Salibi da haka, masu nazarin sun yi nuni da cewa, ana sa ran cewa, ta hanyar bibiyar irin wadannan alamun ciwon Parkinson's ne, za a fara daidaita ciwon shekaru 20 kafin a tabbatar da an kamu da shi. (Tasallah Yuan)