Shugaban Zambia ya tura sojoji su dakile tashin hankali gabanin zabukan dake tafe

CRI2021-08-02 10:24:46

Shugaban Zambia ya tura sojoji su dakile tashin hankali gabanin zabukan dake tafe_fororder_Edgar Lungu

A jiya ne shugaban kasar Zambia Edgar Lungu, ya umarci sojojin kasa da na sama, gami da dakarun tabbatar da zaman lafiya ta kasa, da su taimakawa ‘yan sanda, wajen dakile duk wani tashin hankali da za a iya fuskanta a wasu sassan kasar, gabanin zabukan ranar 12 ga watan Agusta dake tafe.

Shugaban wanda ya bayyana haka a shafinsa na facebook, ya ce, tabbatar da doka da oda, muhimmin aikin yau da kullum ne na ‘yan sanda, amma a wasu lokuta, suna bukatar taimakon wasu bangarori na tsaro. Yana mai cewa, ya dauki wannan mataki ne, don tabbatar da cewa, ba a tsoma baki a harkokin hukumar zaben kasar ba.

Shugaban ya ce, yanzu haka an tura dakarun tsaro zuwa Lusaka, babban binrin kasar, bayan tashin hankali da ya haddasa mutuwar mutane biyu kwanaki biyu da suka gabata. Za kuma a kara tura jami’an tsaro zuwa sauran sassan kasar, idan har bukatar hakan ta taso.

Shugaba Lungu ya kuma bayyana damuwa kan yadda aka kashe mutane yayin da suke kokarin sauke nauyin da kundin tsarin mulki ya ba su. A don haka ya bukaci magoya bayan jam’iyyun siyasa da su kai zuciya nesa.(Ibrahim)

Not Found!(404)