Babban sakataren MDD Antonio Guterres, ya bayyana matukar juyayin mutuwar tsohon shugaban kasar Zambia, Kenneth Kaunda.
A sanarwa da kakakinsa Stephane Dujarric ya fitar, babban sakataren ya bayyana cewa, a wannan lokaci an yi babbar hasara, Guterres ya mika sakon ta’aziyya ga iyalan tsohon shugaban kasar, da gwamnatin kasar da kuma al’ummar kasar ta Zambia.
Ya ce, a matsayinsa na shugaban kasa na farko na kasar Zambia, Kaunda ya kasance babban jigo wajen gwagwarmayar dora kasar kan tsarin demokaradiyya bayan samu ‘yancin da kuma babban dan kishin cigaban Afrika.
Gwamnatin kasar Zambian ta sanar a ranar Alhamis cewa, Kenneth Kaunda, shi ne shugaban kasar Zambia na farko, ya rasu yana da shekaru 97 a duniya. An haifi Kaunda a shekarar 1924, ya jagoranci gwagwarmayar tabbatar da ‘yancin kan kasar Zambia kuma ya jagorancin kasar a matsayin shugaban kasar na farko daga shekarar 1964 zuwa 1991.
Sakataren majalisar ministocin kasar, Simon Miti, ya sanar da mutuwar Kaunda a ranar Alhamis a wani asibitin sojoji, inda ake duba lafiyarsa tun a ranar Litinin a Lusaka, babban birnin kasar. Sai dai Miti bai bayyana dalilin mutuwarsa ba. Amma ofishin Kaunda ya bayyana tun a farkon wannan mako cewa, sakamakon binciken da aka gudanar ya nuna cewa tsohon shugaban kasar yana fama da cutar nimomiya. (Ahmad)