Shugaban kasar Zambia Edgar Lungu, ya yiwa fursunoni 579 afuwa, a wani bangare na bikin tunawa da ranar samun ‘yancin Afirka.
Babban sakataren ma’aikatar kula da harkokin cikin gida na kasar, Masiye Banda ya bayyana cewa, daga cikin fursunonin da aka yiwa afuwa, sun hada da maza 548 da mata 31. Yana mai cewa, yiwa fursunonin afuwa, zai taimaka nesa ba kusa ba, wajen rage cunkoso a gidajen yarin kasar.
A cewarsa, wannan mataki na kara nuna yadda gwamnati ke martaba hakkin dan-Adam, da yadda ake kula da ma tsugunar da masu aikata laifuffuka.
A yau ne dai kasar ta Zambia, za ta bi sahun sauran kasashen Afirka, wajen bikin ranar samun ‘yancin na Afirka.(Ibrahim)