Jiya Talata 27 ga wata, zaunannen wakilin kasar Sin a MDD Dai Bing, ya ce a shirye kasarsa take ta taka rawar gani wajen wanzar da zaman lafiya a kasar Sudan.
Dai Bing ya bayyana cewa, kasar Sin ta shiryawa hada hannu da sauran al’ummar duniya wajen ci gaba da taka rawa a fannin wanzar da zaman lafiya a Sudan.
Wakilin na kasar Sin ya bayyana haka ne yayin taron kwamitin sulhu na MDD kan janyewa da rufe shirin rundunar wanzar da zaman lafiya na hadin gwiwa tsakanin majalisar da kungiyar Tarayyar Afrika wato UNAMID, kamar yadda kudurin MDD mai lamba 2559 ya bukata.
A cewar Dai Bing, tun bayan kafuwarsa, shirin rundunar UNAMID ya taka muhimmiyar rawa wajen tabbatar da tsaro da zaman lafiya a Darfur da ke kasar Sudan, yana mai cewa shi ne irinsa na farko da aka kafa tsakanin hukumomin biyu.
Ya kuma jaddada cewa, hakkin gwamnatin Sudan ne kare fararen hular dake Darfur. Har ila yau, idan ana son cimma zaman lafiya da kwanciyar hankali a Darfur, ya zama wajibi a magance tushen rikice-rikice ta hanyar raya tattalin arziki da inganta walwalar jama’a. (Fa’iza Mustapha)