Shugaban majalisar mulkin kasar Sudan, Abdel Fattah Al-Burhan, ya zartar da wata doka karkashin kundin tsarin mulki, domin kara sabbin mambobi 3 cikin majalisar.
Wata sanarwa da gwamnatin ta fitar, ta ce karkashin tanadin dokar, an nada Al-Hadi Idris da Al-Tahir Abu Bakr Hajar da Malik Agar a matsayin mambobin majalisar mulkin kasar.
Wannan na zuwa ne yayin da ake aiwatar da yarjejeniyar zaman lafiya da aka cimma tsakanin gwamnatin Sudan da kungiyoyi masu dauke da makamai a Juba, babban birnin Sudan ta Kudu, a ranar 30 ga watan Oktoban 2020, wanda ya tanadi damawa da wadanda ke da ruwa da tsaki a tsarin wa’adin gwamnatin wucin gadi, ciki har da mambobin majalisar mulkin kasa da ministoci da majalisar dokoki.
Da nadin sabbin mambobin 3, yanzu adadin mambobin majalisar mulkin ya karu zuwa 14. Bangarorin da suka cimma yarjejeniyar ne ke da alhakin kafa ma’aikatu 7 a sabuwar gwamnatin. (Fa’iza Mustapha)