Kasar Sudan ta bukaci kwararrun kungiyar tarayyar Afrika AU da su taka muhimmiyar rawa wajen shiga tsakani kan batun gina katafariyar matsadar ruwan kasar Habasha ta GERD a tekun Nile.
Shugaban majalisar mulkin Sudan Abdel Fattah Al-Burhan, a ranar Litinin ya gana da ministocin kasashen waje da na noman rani. A yayin taron nasu, an yiwa Al-Burhan karin haske game da cigaban da aka samu a tattaunawar kasashen uku da suka hada da Sudan, Habasha, da Masar game da batun madatsar ruwan da kuma dalilan da suka sanya aka tashi baram-baram a tattaunawar baya bayan nan kan batun.
Yasir Abbas, ministan albarkatun ruwa da noman rani na kasar Sudan, ya ce sakamakon taron ne Sudan ta goyi bayan kungiyar tarayyar Afrika AU da ta taka muhimmiyar rawa wajen jagorantar tattaunawar.
Ministan ya jaddada aniyar Sudan cewa, tattaunawa ce kadai mafita wajen warware takaddamar batun madatsar ruwan ta GERD, kuma idan aka yiwa kowane bangare adalci.(Ahmad)