Masu karatu, ko kuna matukar damuwa sakamakon babban matsin lambar da kuke fuskanta? To, ya fi kyau ku yi barci isasshe. Wani sabon nazari ya nuna mana cewa, yin barci isasshe da dare yana taimakawa wajen kwantar da hankali, da sassauta damuwa, yayin da watakila gazawa wajen yin barci a dare ya kan kara damuwar mutane da kaso 30 cikin 100.
Masu nazarin daga reshen jami’ar California ta kasar Amurka a Berkeley sun kaddamar da rahoton nazarinsu a kwanan baya, inda a cewarsu, sun yi amfani da wasu fasahohin zamani wajen gudanar da nazari kan yadda matasa 18 suke yin barci da kuma damuwarsu. Sun gano cewa, yin barci yana iya rage damuwar mutane sosai, musamman ma yin barci mai zurfi.
Masu nazarin daga reshen jami’ar California ta kasar Amurka a Berkeley sun yi nuni da cewa, sun gano wani sabon amfani da yin barci mai zurfi yake da shi, wato yin barci mai zurfi yana iya kyautata kwakwalwar mutane, ta yadda zai sassauta damuwar mutane a dare guda. Ga alama yin barci mai zurfi, wani nau’in magani ne na musamman wajen rage damuwar mutane.
Ban da haka kuma, masu nazarin sun gano cewa, rashin isasshen barci kan tsananta damuwar mutane. Hoton da aka dauka kan kwakwalwar mutane ya shaida cewa, idan wani bai yi barci da dare ba, to, wani sashen kwakwalwarsa mai kula da sarrafa damuwa ya kan daina aiki baki daya.
Ma iya cewa, idan ba a yi barci da dare ba, to, kwakwalwar mutane kan yi aiki fiye da kima, amma ba a iya hana hakan.
Baya ga nazarin da aka ambato a baya, masu nazarin sun samu sakamako kusan iri daya daga nazarin da suka gudanar kan wasu mutane 30 na daban. Wadanda suka yi barci mai zurfi da yawa da dare, damuwarsu ta kan ragu a kashegari. Har ila yau kuma, wani binciken da aka gudanar kan mutane 280 kan yanar gizo ta Internet ya nuna cewa, ingancin barci da dare da kuma tsawon lokacin barci suna tasiri kan damuwar mutane a kashegari.
Dangane da lamarin, madam Zhang Chuji, wata likita da ke aiki a asibitin Tiantan na Beijing ta yi mana karin bayani cewa, wadanda suke da ciwon damuwa ba safai su kan yi barci yadda ya kamata ba. Watakila za su sassauta damuwarsu ta hanyar kyautata yin barci.
Ban da haka kuma, a wasu kasashe masu arzikin masana’antu, kullum mutane da yawa ba su yin barci yadda ya kamata ba, kana kuma yawan masu kamuwa da ciwon damuwa yana ta karuwa. Watakila akwai wata alaka a tsakanin al’amuran 2. (Tasallah Yuan)