Museveni da Ruto sun bukaci a kafa kungiyar siyasa ta EAC

CRI2021-07-07 11:35:16

Shugaban kasar Uganda Yoweri Musevi, da mataimakin shugaban kasar Kenya William Ruto, sun ba da shawara da a kafa wata kungiyar siyasa ta kungiyar kasashen gabashin Afirka (EAC).

Wata sanarwar da fadar shugaban kasar Uganda ta fitar, yayin bikin aza harsashin gina cibiyar binciken fasahar halittu, da ya gudana a gundumar Wakiso dake tsakiyar kasar, shugaba Museveni ya bayyana cewa, akwai bukatar kasashen Afirka, su fahimci cewa, sai fa sun dunkule waje guda, kafin su tabbatar da samar da makoma mai kyau ga al’ummominsu.

A nasa jawabin mataimakin shugaban kasar Kenya dake ziyara a kasar, William Ruto, ya bayyana cewa, al’ummar nahiyar za su iya kara yin cinikayya, da harkokin kasuwanci, da ma hadewa da juna yadda ya kamata. Kungiyar kasashen gabashin Afirka dai, ta kunshi kasashe guda shida ne, wato, Uganda, da Rwanda, da Kenya da Tanzaniya, da Burundi da kuma Sudan ta kudu.(Ibrahim)

Not Found!(404)