Adadin wadanda suka mutu a ginin da ya rushe a Floridan Amurka ya karu zuwa 36

CRI2021-07-07 11:19:31

Adadin wadanda suka mutu a ginin da ya rushe a Floridan Amurka ya karu zuwa 36_fororder_3e02f5a5022049ca9f70383cd1ac2605

Rahotanni daga kasar Amurka na cewa, adadin wadanda suka mutu, a babban gini mai hawa 12 da ya rushe a wajen jihar Florida dake yankin kudu maso gabashin Amurka, ya karu zuwa 36, bayan kara gano wasu gawarwaki guda 8.

Magajin garin Miami-Dade, Daniella Levine Cava, ta bayyana cewa, ya zuwa yanzu, adadin mutanen da aka tabatar sun mutu, ya kai 36, an kuma gano 26 daga cikinsu. Tana mai cewa, da wannan adadi, akwai mutane 109 da har yanzu ba a kai ga gano su ba.(Ibrahim)

Not Found!(404)