Firaministan kasar Sin ya tattauna da manyan ‘yan kasuwan Birtaniya

CRI2021-07-07 14:34:57

Firaministan kasar Sin ya tattauna da manyan ‘yan kasuwan Birtaniya_fororder_4610b912c8fcc3ceb36c0d5d374d1280d53f20c5

Firaministan kasar Sin Li Keqiang, ya tattauna da manyan ‘yan kasuwar Birtaniya, inda ya bayyana fatan karfafa aminci da hadin gwiwa a tsakaninsu domin moriyar juna da kyautata huldar dake tsakanin kasashensu.

Da yake bayani game da yanayin rashin tabbas da duniya ke ciki, Li Keqiang ya ce, Sin da Birtaniya, mambobi ne na dindindin a kwamitin sulhu na MDD, haka kuma masu karfin tattalin arziki a duniya, wadanda kuma ke da karfin kare zaman lafiya a duniya da inganta ci gaba da kare tsarin huldar kasa da kasa.

A nasu bangaren, ‘yan kasuwan Birtaniya sun ce Sin muhimmiyar abokiyar hadin gwiwar tattalin arziki da cinikayya ce ga Birtaniya, haka kuma suna girmama kasuwar kasar Sin tare da imani da ci gabanta.

Sun kara da cewa, akwai dimbin damarmakin hadin gwiwar moriyar juna tsakanin kasashen a fannonin da suka shafi harkokin kudi da hidimomi da aikin gona da kiwon lafiya da ilimi da ababen more rayuwa, inda suka ce bangarorin kasuwanci na Birtaniya na sa ran kara inganta dangantakar cinikayya da zuba jari da kasar Sin, da zurfafa hadin gwiwa da raya dangantakar kasashen biyu. (Fa’iza Mustapha)

Not Found!(404)