Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
CIIE ya kara nuna kudirin kasar Sin na kara bude kafarta
2020-11-11 20:01:51        cri
Mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Wang Wenbin, ya bayyana cewa, sakamakon da aka cimma a fannin hadin gwiwar tattalin arziki da cinikayya a bikin baje kolin kasa da kasa na kayayyakin da ake shigowa da su cikin kasar Sin (CIIE) da aka kammala a birnin Shanghai, ya dara na shekaru biyun da suka gabata, matakain da ya haifar da kyakkyawan sakamako, kana ya alamta kudirin kasar na kara bude kofofinta, da yin hadin gwiwa da samun nasara tare.

Wang Wenbin ya jadadda cewa, muddin kasashe suka martaba manufar bude kofa da yin hadin gwiwa yadda ya kamata, hakika za a iya magance tasirin annobar COVID-19 nan da nan, har ma a kai ga dawo da tattalin arzikin duniya bisa turba bayan annobar.

A yau ne kuma zaunannen kwamitin majalisar wakilan jama'a, ya tattauna tare da amincewa kan dokar soke mambobin majalisar dokokin yankin musamman na Hong Kong wadanda suke yunkurin rarraba kasar Sin. Da yake karin haske yayin taron manema labaran da aka saba shiryawa, Wang Wenbin, ya bayyana cewa, an yanke shawarar ce, domin martaba da ma inganta tsarin nan na "kasa daya, tsarin mulkin iri biyu", da aiwatar da muhimmiyar dokar yankin Hong Kong da ka'idojin dokar tsaron kasa mai nasaba da yankin Hong Kong, da sauran ka'idojin doka da su ma suka wajaba a kiyaye a yankin na Hong Kong da sauran dokoki dake kunshe cikin kundin dokokin yankin musamman na Hong Kong na kasar Sin. (Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China