Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sin ta soki matakin Amurka na ayyana karin wasu kafofin watsa labaru a matsayin ofisoshin diflomasiyyar waje
2020-10-22 21:15:18        cri
Mai magana da yawun ma'aikatar wajen kasar Sin Zhao Lijian, ya yi suka da kakkausar murya game da matakin Amurka, na ayyana karin wasu kafafen watsa labarun Sin guda 6 dake Amurka, a matsayin ofisoshin diflomasiyyar waje.

A jiya Laraba, 21 ga watan nan ne Amurka, ta ayyana wasu kafofin watsa labarai na Sin 6 dake sassan Amurkar, a matsayin ofisoshin diflomasiyyar waje, wanda hakan zai sauya matsayin su na damar gudanar da ayyuka yadda ya kamata.

Zhao Lijian wanda ya bayyana hakan a yau Alhamis, yayin taron manema labarai da aka saba gudanarwa, ya ce wannan wani sabon mataki ne na siyasa da Amurka ke aiwatarwa, domin kuntatawa kafofin watsa labarai da 'yan jaridar Sin. Kuma mataki ne da Sin ta yi matukar Allah wadai da shi.

Zhao Lijian ya kara da cewa, a 'yan shekarun baya bayan nan, gwamnatin Amurka na ta dorawa kafofin watsa labarai da 'yan jaridar Sin dake aiki a Amurkan takunkumi, da matsin lamba ba gaira ba dalili, ta kuma tsananta wajen aiwatar da matakan nuna wariya da muzgunawar siyasa kan kafofin na Sin.

Bisa hakan ne kuma, Sin ke kira ga Amurka da ta gaggauta sauya matsaya, ta gyara kura-kuran ta, ta kuma dakatar da matsin lamba irin na siyasa maras dalili kan kafofin watsa labarai na Sin. (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China