Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sin ta mayar da martani game da matakin Amurka na ayyana wasu kafofin watsa labarun ta a matsayin ofisoshin harkokin waje
2020-10-27 10:00:15        cri
Kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Zhao Lijian, ya ce sakamakon yadda gwamnatin Amurka ta ayyana wasu kafofin watsa labarun Sin guda 6, a matsayin ofisoshin harkokin waje, ita ma Sin ta umarci wasu rassan kafofin watsa labaran Amurka dake aiki a Sin, da su gabatar mata wasu bayanai cikin mako guda.

Mr. Zhao ya ce gwamnatin Sin, ta umarci kafofin da suka hada da "ABC", da "The Los Angeles Times", da "Minnesota Public Radio", da "Bureau of National Affairs", da "Newsweek" da "Feature Story News", da su gabagar da rubutattun bayanai game da ma'aikatansu, da hada-hadar kudadensu, da yanayin ayyukansu, da muhallansu a Sin.

Jami'in ya kara da cewa, a baya-bayan nan gwamnatin Amurka ta kakabawa wasu kafofin watsa labarai na Sin, da ma'aikatansu dake aiki a Amurka takunkumai ba gaira ba dalili, da nufin hana su gabatar da ayyukan su kamar yadda suka saba, matakin da ke sakawa ana nuna musu wariya da danniya irin ta siyasa.

Karkashin irin wadannan matakai ne, Amurkan ta ayyana wasu kafofin watsa labarun Sin guda 6 a matsayin ofisoshin harkokin waje, matakin da tun a makon jiya, Sin ta nuna matukar adawa da shi, tana kuma mai kira ga Amurka da ta gaggauta janye shi. (Saminu Alhassan)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China