![]() |
|
2020-11-11 19:32:10 cri |
Shawarar ta bayyana karara cewa, mambobin majalisar dokokin yankin musamman na Hong Kong, sun yayata ko goyi bayan neman 'yancin kan Hong kong", ko neman kasashen ketare ko wasu daga ketare su tsoma baki a harkokin yankin musamman na Hong Kong, ko aikata wasu ayyuka dake da hadari ga tsaron kasar. Idan har suka gaza cimma ka'idoji ko sharudda na martaba muhimman dokokin yankin musamman na Hong Kong na jamhuriyar jama'ar kasar Sin da martaba yankin musamman na Hong Kong na jamhuriyar jama'ar kasar Sin, aka kuma tabbatar bisa doka, to za a iya soke matsayinsu na zama mamba a majalisar dokoki ba tare da bata lokaci ba. (Ibrahim)
| ||||
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China