Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Babban yankin Sin na goyon bayan babbar jami'ar gudanarwa ta Hong Kong a kokarin da ake yi na shawo kan kalubalen yankin
2019-09-03 19:31:32        cri
Kakakin ofishin majalissar gudanawar kasar Sin mai lura da al'amuran Hong Kong da Macao Mr. Yang Guang, ya ce mahukuntan babban yankin Sin, na goyon bayan babbar jami'ar gudanarwa ta yankin Hong Kong Carrie Lam, a kokarinta na aiki tare da sauran al'ummun yankin, wajen warware tarin matsalolin tattalin arziki da na zamantakewar al'umma dake shafar yankin.

Yang Guang, ya yi wannan tsokaci ne a Talatar nan, yayin wani taron manema labarai da ya gudana, inda ya ce tarzomar dake wakana a yankin na da nasaba da wasu matsaloli dake da dogon tarihi, wadanda kuma ke bukatar sahihan hanyoyin warware su.

Jami'in ya kara da cewa, gwamnatin babban yankin Sin, na goyon bayan yunkurin Lam, da gwamnatinta, a fannin ci gaba da tattauna matakan shawo kan matsalolin yankin tare da al'ummarsa na sassan rayuwa daban daban, ciki hadda matasa. (Saminu Hassan)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China