Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Bangarori daban-daban a Hong Kong sun goyi-bayan kudurin da majalisar NPC ta zartas
2020-05-30 17:34:51        cri
Daga ranar 24 zuwa 31 ga wata, bangarori daban-daban masu goyon-bayan kafa dokar kiyaye tsaron kasa a yankin Hong Kong, sun kafa rumfuna a sassa da dama na yankin, inda suka tattara sa hannun jama'a na goyon-bayan lamarin.

Da maraicen ranar 28 ga wata, a wajen zama na uku na majalisar wakilan jama'ar kasar Sin NPC karo na 13, aka zartas da kudurin majalisar game da kafawa gami da inganta dokar kiyaye tsaron kasa ta yankin musamman na Hong Kong da kuma tsarin aiwatar da ita. Bayan samun labarin, akwai mazauna yankin Hong Kong da dama wadanda suka bayyana goyon-bayansu kan irin wannan kuduri.

Wata 'yar yankin Hong Kong ta bayyana cewa, tana fatan kasar Sin za ta kara samun karfi da wadata, kuma ba sa bukatar duk wani shisshigi daga kasashen waje. Tana mai cewa, in dai kasar ta samu karfi da wadata, to yankin Hong Kong ma zai bunkasa.

Zuwa tsakar ranar jiya 29 ga wata, adadin mutanen Hong Kong da suka sa hannu domin mara baya ga kafa dokar kiyaye tsaron kasa ta yankin, ya zarce miliyan 2.12, adadin da ya karu da dubu 270 idan aka kwatanta da na tsakar ranar 28 ga wata.

Har wa yau, mutanen bangarori daban-daban na Hong Kong sun bayyana cewa, za su bada cikakken hadin-kai domin gaggauta kammala aikin kafa dokar, ta yadda za'a kiyaye tsaron kasa da na yankin.

A nata bangaren, sakatariyar shari'a ta yankin Hong Kong, madam Teresa Cheng Yeuk-wah ta ce, zartas da irin wannan doka da majalisar wakilan jama'ar kasar Sin ta yi, ya dace da halin da ake ciki kuma ya yi daidai bisa kundin tsarin mulkin kasa, kana ya dace da babbar doka ta yankin na Hong Kong. Ta ce, tabbatar da tsaro ya zama wajibi ga bunkasar wata kasa mai dorewa. Inda ta ce, in dai an samu tsaro mai inganci da kwanciyar hankali, za'a iya aiwatar da manufar "kasancewar kasa daya mai tsarin mulki biyu" cikin dogon lokaci, kuma yadda ya kamata. (Murtala Zhang)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China