Kasar Sin ta taya Alassane Ouattara murnar sake zama shugaban kasa
Kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin, mista Wang Wenbin, ya bayyana a yau Laraba cewa, kasar Sin tana taya shugaban kasar mai ci Cote d'Ivoire, Alassane Ouattara murnar sake lashe babban zaben kasar. A cewar kakakin, kasar Sin da kasar Cote d'Ivoire na da hulda mai kyau. Kana a nan gaba kasar Sin na son karfafa hadin gwiwa da Cote d'Ivore, don kara yaukaka huldar dake tsakanin kasashen 2. (Bello Wang)
Labarai masu Nasaba